Taskar Labarai Tsaro

Yadda Ango Yayi Shahada Yayin Hana Yan Ta’adda Daukar Matarsa Mai Ciki

Yadda Ango Yayi Shahada Yayin Hana Yan Ta'adda Daukar Matarsa Mai Ciki

A ranar da al’amarin zai faru, Auwal ya dauka amaryarsa Rabiatu inda ya kai ta dakin haihuwa dake Kwatas din Masukwani saboda laulayin ciki da take fama da shi.

Zuwa bayan isha’i duk a ranar, ‘dan uwansa Rabi’u ya ziyarcesa tare da matarsa Aisha.

Sun dade suna tattaunawa a kan rayuwa har sai da Rabi’u yace za su koma gida da matarsa.

Ba su dade da tafiya ba inda suka bar Auwal kwance a kan tabarma yayin da amaryarsa ke kwance kusa da shi, kawai ‘yan bindiga suka bayyana tare da zagaye gidan. Ba su yi harbi ba a kofar shiga saboda dare bai yi sosai ba.

Sun bai wa Auwal umarni amma yayi shiru, a lokacin da suka fusata sai suka ce zasu tafi da Auwal tare da matarsa. Nan kuwa Auwal yace babu inda zasu je. Ya tashi ya rufe hanyar shiga dakin amma cike da rashin sa’a suka harbesa a hannu, Leadership ta ruwaito.

Mummunan harbin ya ragargaza kasusuwan hannun Auwal. ‘Yan bindigan sun yi yunkurin daukar matar Auwal amma ya hana inda yace babu inda zasu je. A take suka harbe shi sau uku a ciki kuma ya fadi cikin jini. Bayan nan suka tafi da matar Auwal.

‘Dan uwan Auwal, Barde, yana cikin dakinsa yayin da lamarin ke faruwa amma ba shi da kwarin guiwar fitowa har sai da ya fahimci ‘yan bindigan sun fice. A nan ya dinga ihu yana cewa sun kashe Danlami (Auwal).

Duk da halin da Auwal ke ciki, an ji yana cewa

“Ku dauke ni, sun tafi da matata” har ta kai ga baya iya cewa komai.
Wani makusancin Auwal ne ya bada labarin yadda ‘yan bindiga suka kutsa garin Jere dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka kashe ango tare da yin a won gaba da matarsa mai tsohon ciki.

Aika Da Wannan Labarin: