Al'umma

Yadda aka binne gawar Deborah Samuel cikin hawaye a Niger

A yau ne aka binne gawar marigayiya Deborah Samuel dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari dake jihar Sokoto a garin su dake Tungan Magajiya dake karamar hukumar Rijau a jihar Neja a yau cikin cece-kuce.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake zargin Gwamnatin Jihar Sakkwato ta dage cewa a ajiye gawar a dakin ajiyar gawarwaki har sai ta kammala shirye-shiryent a kan lamarin.

Yan uwan ta dalibai ne suka jefe Deborah da duwatsu har lahira a ranar Alhamis, bisa yin kalaman batanci a wani group na WhatsApp.

An tattaro cewa marigayiyar ta kasance tare da yan uwa a Sakkwato tun tana makarantar firamare kafin rasuwar ta.

An tattaro cewa a lokacin da ake jigilar gawar Deborah zuwa gida domin binne ta, wani jami’in gwamnatin jihar Sokoto ya yi kira da a mayar da gawar a matsayin ta gwamnati.

Gwamnati ta bukaci iyalan da su ajiye mamaciyat a dakin ajiyar gawa har sai an kammala shirye-shiryen binne ta.

Sai dai iyayen ba su amince da matakin gwamnati ba, yayin da suka dage cewa za a binne gawar yar su a yau.

Arewa Times Hausa ta samu cewa tun da labarin faruwar lamarin ya kai ga iyayen Deborah, mahaifiyar ta sume a yayin da mahaifin ke cikin bacin rai da radadi.

Da yake mayar da martani, Fasto na iyali mai kula da ECWA ta daya a Tunga Magajiya, Fasto Emmanuel Maaji ya bayyana cewa ‘yan uwa sun dage cewa a yi jana’izar ‘yar su a yau, sabanin yadda gwamnatin jihar ta ce ta jira har sai ta kammala nata tsarin.

A cewar shi, iyayen ba su ji dadin yadda lamarin yake ba, kuma ko da gwamnati na shawo kan lamarin.

Malamin ya ce an dawo da gawar marigayin gida ne a cikin motar haya ba motar gwamnati ba.

Maaji ya cigaba da cewa gwamnati ta yi waya ne kawai ta ce ba daidai ba ne ‘yan uwa su dauki gawar haka ba tare da an sanar da su ba. Sun ce bai kamata a binne gawar ba domin gawar ta gwamnati ce ba ta iyali ba. Sun ce su sanya gawar a dakin ajiyar gawa.

Back to top button