Tsaro

Yadda Ɓarayi suka yankewa wani ɗan Achaba hannaye, suka ƙwace dukiyar shi

Inna Lillahi Wa’inna Alaihi Rajee’uun!

Kamar yadda kuke gani a cikin wannan hoton dake a sama, wani bawan Allah ne yan ta’adda masu sace-sace suka yanke mai hannuen ahi sannan suka tafi dukiyar shi saboda rashin imani.

Hoto na farko dake kgani an dauke shi ne wani lokaci kafin faruwar wannan mummunan al’amari lokacin da zai fita wurin kasuwancin shi.

Advertisement

Haka zalika hoton kuma na biyu a assibiti ne aka dauke bayan yan ta’adda sun yanke mai hannaye sannan sun karbe babur din shi da kudin dake tare da shi a lokacin.

Yahaya Galadima matashi mai shekaru 25 dake kwance a assibitin (Specialist Hospital Lafia/Nasarawa) yana neman addu’ar ku. Jiya ya fita kasuwa wurin harkar shi ta achaba/kabu-kabu, barayi suka tare shi suka karbe mai babur da kudi kuma suka datse hannayen shi har abada.

Yan masu albarka muyi ta addu’a, sannan mu turawa sauran mutane wannan ta’addancin da aka yiwa wannan bawan Allah mu taahi duka da addu’o’in zama lafiya da karshe mai kyau.

Advertisement