Tsaro

Yadda ƴan bindiga suka kashe mutane 21 a Zamfara bayan sun karbi haraji miliyan ₦40

Wasu yan bindiga a jihar Zamfara sun kai hari a unguwar Nasarawar Mai-fara da ke karamar hukumar Tsafe, inda suka kashe fiye da mutane 20.

A baya dai yan bindigar sun sanya harajin Naira miliyan ₦40 ga mutanen yankin da lamarin ya shafa. Wani manomi daga yankin yace an binne wadanda harin ya rutsa da su a daren Juma’a.

A cewar shi, yan bindigar kafin su kai harin, sun zo wurin al’umma inda suka bukaci jama’ar yankin da su tara Naira miliyan ₦40 idan suna bukatar zaman lafiya.

Advertisement

Jama’ar yankin sun yi biyayya kuma sun mika kudin ga yan bindigar. Duk da haka, “ sun zo suka mamaye al’ummar mu. Sun kashe sama da mutane 21, ”inji shi.

Yace “abin da ya fi baqin ciki shine bayan kashe mutanen mu, bayan kwana 2 ne suka ba mu damar daukar gawawwakin mu shirya su don binne su.”

Wani dan unguwar da ya tsira da kyar, yace da shiga cikin al’ummar, yan bindigar sun nufi Masallaci inda suka bude wuta kan Musulmin da ke Sallah.

Yace ‘yan banga na yankin sun tunkari yan bindigar, nan da nan bayan harin da aka kai wa masu ibada.

“Lokacin da rikicin ya tsananta sai da muka kira jami’an tsaro amma sai da suka dauki awanni 2 kafin su zo. Harbin bindigogi ne tsawon wadannan awanni 2,” inji shi.

Yace an kashe mutane 11 a harin na Masallacin, 4 sun jikkata yayin da aka sace mata da yawa.

A wani labarin makamancin haka, mazauna garin Tofar Magami dake karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara sun ‘yanto tare da barin ‘yan bindigar sun mamaye al’umma.

Wani tsohon mazaunin al’ummar da yanzu haka ke gudun hijira, ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa babu wani dan asalin garin a yanzu yayin da duk suka gudu.

Yan bindigar sun mayar da wurin sansaninsu,” in ji shi.

Yan bindigar yanzu haka suna zaune a gidajen wadanda suka gudu suna wulakanta mu. Ya kai matsayin da za su iya yi wa mace fyade a gaban mijinta,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara; SP Muhammad Shehu ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa sun samu damar ziyartar al’ummar da abin ya shafa tare da jajanta wa wadanda abin ya shafa.

Yace an hada tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa domin ziyartar al’umma kuma ana kokarin daukar dabarun da ya dace na dakile hare-haren ‘yan bindiga a cikin al’umma.

Advertisement