Laifuku

Ya lallaɓi uwa ta kuma ya kashe ta bayan yayi alkawarin taimaka mata, ita ba karuwar shi ba ce – Suleimon

Sulaimon Yekeen, dan matar mai shekaru 52 da mijin ta ya rasu, A’ishatu Yekeen, wadda a kwanakin baya wani da ake zargin mai tsafi ne ya kashe ta a jihar Osun, ya bayyana yadda aka yaudari mahaifiyar shi da kuma kashe mahaifiyarta ga wakilin jaridar The Punch.

Nafiu, daya daga cikin mutane ukun da ake zargin sun kashe matar, yayi ikirarin cewa yana soyayya da marigayiyar a baya kuma ya yaudare ta zuwa gidan shi bayan abokin nasa shi ma ya nuna yana son saduwa da ita.

A lokacin ne aka kashe ta don yin tsafin kuɗi.

Sai dai Sulaimon Yekeen dan marigayiyar ya musanta maganar da Nafiu yayi inda yace yana soyayya da mahaifiyar ta.

A cewar Sulaimon Yekeen, wanda ake zargin wani tsohon abokin dangin su ne da ke zuwa gidan su bayan ya tashi daga Legas tun kafin rasuwar mahaifin su.

Nafiu ya bar yankin su ne a wani lokaci bayan ya saci wasu jalkokin man ja na uwargidan shi ya kuma kona mata dakin ta saboda kada asirin shi ya tonu.

Sulaimon Yekeen ya bayyana cewa, Nafiu, wanda Malamin addinin Musulunci ne, yayi alkawarin taimaka wa mahaifiyar shi ta shirya wasu abubuwa da za su taimaka wajen hana yar uwarbta shan giya fiye da kima, kuma wadannan su ne kayan da mahaifiyar shi ta tafi karba kafin a kashe ta aka yanke gawar ta domin yin tsafin kuɗi.

Advertisement