Labarai

Yaƙin Lebanon Yaƙin Duniya Na III Ne Da Gwamnatin Joe Biden Ta Ɗauki Nauyi

Ibrahim Fraihat, farfesa na warware rikice-rikice na kasa da kasa a Cibiyar Nazarin Digiri na Doha dake ƙasar Qatar, ya ce “An sa ranar yaduwar yakin Isra’ila a Gaza zuwa Lebanon amma abin da ba a yi tsammani ba shi ne adadin wadanda suka mutu na kwana guda.”

“An kashe kusan fararen hula fiye da 550 a rana guda. Babban abin mamaki shi ne shiru da gwamnatocin kasashen yamma suka yi. Babu wani bayani na hakika, babu wani matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na dakatar da hare-haren da take kaiwa,” kamar yadda ya shaida wa Al Jazeera.

Fraihat ya ce shugaban Amurka Joe Biden “yana ba da tallafi ga wannan yakin”.

“Wannan shi ne yakin duniya na III da Amurka ta ba da tallafi a lokacin shugabancin Joe Biden bayan Ukraine da Gaza. Ya kara da cewa yana aikewa da karin sojoji da karin makamai zuwa Isra’ila, don haka ayyuka suna magana da kansu.”

Fraihat ya kuma ce yakin da ake yi a Labanon ya samo asali ne sakamakon gazawar Biden a Gaza “saboda ya kasance yana goyon baya da kuma karfafa Isra’ila a can wajen kashewa da kawar da Falasdinawa”.

“Sakataren harkokin wajen Joe Biden, Antony Blinken, bai cimma komai ba a ziyararsa bakwai a yankin gabas ta tsakiya ba, ko da musayar fursunoni. Kuma wa ya sani, watakila akwai yaƙi na huɗu da ke zuwa kafin Joe Biden ya bar ofis, ”in ji shi.