Tsaro

Yaƙi: Sojojin Ukraine sun kashe Manjo Janar Andrei Sukhovetsky na Rasha

An kashe Manjo Janar na kasar Rasha Andrei Sukhovetsky, a cewar CNN.

An kashe Sukhovetsky ne a lokacin da ake gwabza fada a Ukraine, a cewar wata sanarwa daga gwamnatin birnin Novorossiysk.

A cikin sanarwar, gwamnatin kasar ta ce Sukhovetsky, wanda shi ne mataimakin kwamandan runduna ta 41 ta hadin gwiwa ta sojojin kasa ta Rasha, ya mutu “a lokacin da yake aikin yaki a wani samame na musamman a Ukraine.”

Advertisement

Sanarwar ta ce, a baya ya taba yin aikin sojan kasar Rasha a lokacin da ake kai hare-hare a yankin Arewacin Caucasus da kuma Siriya.

A halin da ake ciki dai sojojin na Ukraine sun yi ikirarin cewa sun yi nasarar fatattakar wani rukunin sojojin Rasha tare da kashe kwamandan su Kanar A. Zakharov.

An ce sun samu nasarar ne a garin Brovary dake arewa maso gabashin Kyiv.

Advertisement