Tsaro

Yaƙi: Ku ne gaba idan Rasha ta rushe Ukraine – Zelensky ya yiwa Amurka da NATO kashedi

Shugaban Ukraine Volodymr Zelensky ya aike da gargadi ga kasashen yammacin duniya cewa ƙasar Rasha za ta bi su da zarar ta gama da kasar Ukraine.

Shugaban na Ukraine ya cigaba da cewa yakin ba zai tsaya a Ukraine ba kawai, yana mai jaddada cewa harin da Rasha ke kaiwa Ukraine ba zai shafi kasar shi kadai ba har ma da sauran kasashen duniya.

Da yake magana da ABC World News a daren Litinin, shugaban yayi kira ga NATO da Amurka da su tabbatar da sararin samaniyar Ukraine. ‘Ba ma sarrafa sararin samaniyar mu’, inji shi. Zelensky ya kara da cewa yana da imani sosai ga shugaban Amurka, Joe Biden da kuma ikon shi na dakatar da kashe yan Ukraine da lalata dukiyoyin su. Ya kara da cewa shugabannin Amurka na iya kokarin kare kasar shi.

Advertisement

Ku tuna cewa Amurka da NATO sun ba da sanarwar cewa ba za a kafa wani yanki na tashi da saukar jiragen sama a Ukraine ba, tare da tabbatar da cewa suna da alhakin hana barkewar yakin.

A daya hannun kuma a baya kasar Rasha ta fitar da wani gargadin cewa duk kasar da ta yanke shawarar kafa yankin tashi da saukar jiragen sama a Ukraine, za a dauki ta a matsayin mai shiga cikin rikicin soji.

Menene ra’ayinku kan wannan ikirari na shugaban kasar Ukraine?

Advertisement