Tsaro

Yaƙi: An sake kashe wani Laftanar-Janar na Rasha a Ukraine

An kashe wani Laftanar-Janar na kasar Rasha, Yakov Rezantsev, a Ukraine.

A cewar BBC, ma’aikatar tsaron Ukraine ta ce an kashe Rezantsev a wani hari da aka kai a sansanin sojin sama na Chornobaivka, da ke kudancin birnin Kherson na Ukraine jiya Juma’a.

Laftanar-Janar aka kashen shi ne kwamandan runduna ta 49 ta hadin gwiwa ta Rasha.

Rezantsev shi ne Laftanar Janar na biyu, wanda aka ce an kashe jami’in da ya fi kowanne matsayi tun bayan yakin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine a watan jiya.

Ku tuna cewa a makon da ya gabata Ukraine ta ce ta kashe Laftanar-Janar Andrei Mordvichev na Rasha yayin wani hari da aka kai a filin jirgin sama a kudancin kasar.

An fara gwabza yaki tsakanin Rasha da Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayar da umarnin mamaye kasar Ukraine bisa sabanin da aka samu kan wasu batutuwan siyasa.

Ya zuwa yau, an riga an sami asarar rayuka da dama.

Advertisement