Wasanni

World Cup 2022: Kamaru Ta Dakatar Da Onana Daga Gasar Cin Kofin Duniya Da Ke Gudana A Qatar

An kori Andre Onana, wanda ya kasance mai tsaron raga na farko na Kamaru, daga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da ake yi a Qatar saboda dalilai na ladabtarwa bayan takaddama da kocin kungiyar, Rigobert Song.

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta ce an dakatar da dan wasan mai shekaru 26 na wani dan lokaci daga tawagar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata. Dakatarwar za ta ci gaba har zuwa sauran gasar.

Hukumar ta ce ta bai wa Onana umarnin komawa Milan, inda mai tsaron ragar ke taka leda a Inter Milan.

Advertisement
Advertisement