Wasanni

World Cup 2022: Ingila Ta Ci Iran 6-2

A ranar Litinin da yamma Ingila ta doke Iran a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 a Qatar.

Ingila samu nasara akan Iran da ci 6-2 a filin wasa na Khalifa International Stadium.

Kwallaye biyu da Saka suka ci da Jude Bellingham da Raheem Sterling da Marcus Rashford da Jack Grealish kowanne ya ci wa Ingila nasara a kan Iran.

Mehdi Taremi ne ya ciwa Iran kwallayen biyu a karawar.

Nasarar na nufin Ingila a yanzu ta zama ta daya a rukunin B da maki 3 a wasa daya.

Advertisement