Wasanni

Word Cup 2022: Cin Da Ya Buɗe Wasa Da Bai Isa Ba, Yayin Saudiyya Ta Lallasa Argentina Ci 2-1

Kwallon farko da Lionel Messi ya ci wa Argentina a gasar cin kofin duniya ta FIFA 2022 bai isa ba yayin da Saudi Arabiya ta zo daga baya ta doke su da ci 2-1.

Dan wasan gaba na Paris Saint-Germain ya sauya bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 10 inda ya fara kamfen din shi cikin haske, kafin rashin nasara.

Haƙiƙa ya kasance babban abin mamaki ga tsoffin zakarun duniya waɗanda ba su yi rashin nasara ba a gasar cin kofin duniya da suka ci na farko tun 1958.

Advertisement