Siyasa

Wike Ya Sake Caccakar Atiku, Yace Ƴan Najeriya Ba Za Su Zaɓi Ƴan Takarar Ɓangaranci Ba

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya bukaci ‘yan Najeriya da su zabi wanda zai jagoranci Najeriyar zuwa ga cigaba, maimakon zaben shugaban kasa don wani ya ki ba a zaben shugaban kasa na 2023.

Wike ya bayyana haka ne a wani bikin kaddamar da hanya a yankin Emohua na jihar Ribas a ranar Litinin yayin da yake mayar da martani game da wani tsokaci da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar yayi.

A baya-bayan nan Atiku a jihar Kaduna a wani taro yace ‘yan Arewa na bukatar dan Arewa irin shi ba Yarbawa ko dan kabilar Ibo ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayar da mai magana da yawun kungiyar dattawan Arewa NEF, Hakeem Baba-Ahmed, yayi masa a yayin wani taron tattaunawa da kwamitin hadin gwiwa na Arewa da aka gudanar a jihar Kaduna.

Amma da yake mayar da martani a ranar Litinin, Wike yace, “Bai isa a ce kar ku zabi dan kabilar Ibo ko Yarbawa ba, amma abin da muke bukata shi ne mu zabi wanda zai jagoranci Najeriya zuwa ga cigaba.”

Advertisement