Siyasa

Wata tsohuwa mai shekaru 102 ta bayyana aniyar zama shugaban Najeriya a 2023

Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, jama’a da dama na ta tofa albarkacin bakinsu game da burinsu na siyasa na karbar mukamin shugaban kasa ko na gwamna a Najeriya.

A cikin wadannan mutane akwai wata tsohuwa mai shekaru 102 mai suna Amb. Nonye Josephine Ezeanyaeche.

Amb. Nonye Josephine ta bayyana aniyar ta a bainar jama’a na tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zaben 2023.

Advertisement

Amb. Nonye Josephine Ezeanyaeche wanda aka fi sani da ‘Living Legend’ ko kuma ‘Mama Africa’ ita ce ta kafa kungiyar muryar manyan ‘yan Najeriya.

Amb. Nonye ‘yar Aguata, jihar Anambra ta bayyana aniyar ta da baki a lokacin da ta ziyarci tawagar gudanarwar gidan talabijin din mai farin jini; Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA).

Mama Africa ta bayyana cewa shirinta na tsayawa takarar shugaban kasa a Najeriya ya zama dole domin ba ta ga wani sahihin dan takara da aka bayyana aniyarsa ta shugabancin kasar a halin yanzu ba.

Amb. Noonye ta bayyana cewa tana da tsare-tsare masu kyau ga Najeriya sannan ta bayyana shirinta na tsayawa takarar shugabancin Najeriya idan matasan Najeriya ba su shirya ba.

Advertisement