Al'umma

Wata Mata Ta Ki Karbar Motar Da Dan Ba Ta A Ranar Birthday Din Ta Bisa Zargin Dan Damfara Ne

Wata mata ta girgiza mutane da yawa bayan ta ki amincewa da kyautar mota da danta ya yi mata a ranar haihuwar ta saboda ta zarge shi da laifin zama dan damfarar yanar gizo mai suna yahoo boy.

A cikin wani faifan bidiyo da Arewa Times Hausa ta gani a yanar gizo, matashin ya yi kamar ya shiga damuwa lokacin da mahaifiyar shi ta ce ya shiga haramtacciyar mu’amala ne dalilin da ya sa zai iya sayen motar.

Ta zarge shi da cewa ba shi da aiki saboda har yanzu tana zaune a cikin tarkace kuma a ce yanzu ya saya mata babbar mota.

Advertisement

Ta yi barazanar lalata motar idan yaraon bai dauke ta ba saboda ta kira shi mutumin da bai kamata ya iya sayen irin wannan motar ba.

Advertisement