Laifuku

Wata Mata Ta Cinnawa Mahaifin Ta Mai Shekaru 85 Da Mahaifiyar Ta Mai Shekara 80 Wuta

Domin misali

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta fara gudanar da bincike kan halin da ake ciki game da tu’ammali da miyagun kwayoyi tare da kona wani dattijo mai shekaru 85 da matar shi ‘yar shekara 80 da diyar su mai shekaru 52 da haihuwa ta yi.

An tabbatar da mutuwar dattijon a asibitin da aka garzaya da su, yayin da matar ta kasance a sume.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar wa da jaridar Tribune Online faruwar lamarin.

Advertisement

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba a Estate Gate Estate da ke unguwar Lusada a Okokomaiko, daura da babbar hanyar Legas zuwa Badagry.

An tattaro cewa Aleremolen Izokpu mai shekaru 52 ta bai wa iyayen ta Pa Michael Izokou mai shekaru 85 da matar shi Priscilla mai shekaru 80 da haihuwa kwaya.

Wadda ake zargin da ta gudu daga wurin da lamarin ya faru, bayan ta kona iyayen ta biyu da ke barci.

Daya daga cikin ‘yan’uwan wanda ake zargin, Akugbe Izokou ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda bayan daya daga cikin kanwar shi ta sanar da shi ta wayar tarho.

Hundeyin ‘yan sanda ya shaida wa Tribune Online cewa “Bayanan da aka samu daga sashin DPO Okokomaiko sun nuna cewa a ranar 01/12/22 da misalin karfe 09:00 ne wani ya kai rahoto a ofishin cewa a ranar 30/11/22 da misalin karfe 15:00 na safe. Ya samu kiran waya daga kanwar shi, wata Osemudiame Izokpu cewa kanwar su mai suna Aleromolen, mai shekaru 52, ta shayar da iyayen su miyagun kwayoyi, daya Micheal Izokou, mai shekaru 85 da kuma Priscilla Izokpu, mai shekaru 80, kuma ta banka musu wuta a lokacin da suke barci.”

“Jami’an tsaro ne suka ziyarci wurin. An kuma ziyarci asibitin inda aka duba wadanda suka jikkata da gawar, aka dauki hotuna tare da ajiye gawar a dakin ajiye gawa na Asibitin Badagry.

Hundeyin ya kuma bayyana cewa, an zage damtse wajen cafke wanda ake zargi da gudu.

Advertisement