Alaƙa

Wata Mata Ta Cakawa Mijinta Wuka Ya Mutu, Ta Yanke Azzakarin Shi

An zargin wata mata Florencia Amado Cattaneo da yanke al’aurar mijinta tare da daba masa wuka har lahira. Pedro Federico Zarate, mijin nata marigayi mai busar kaho, an gano ya mutu a gidan ma’auratan da ke yankin Altos de San Lorenzo na kasar Argentina.

Jaridar Mail Online ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun kama wadda ake zargin mai shekaru 41 tare da mika ta domin auna lafiyar kwakwalwa dangane da mumunan kisan da ake zargin ta da shi.

Baya ga yanke al’aurar mijinta, ta kuma binne wuka a cikin kwallan idon shi. An gano wanda aka kashe da wuka da aka binne a idon shi kuma aka yanke al’aurar shi.

Advertisement

An tsare wadda ake zargin, kwararriyar ilimin halayyar dan adam ce a ranar 11 ga watan Janairu bayan ta tsere zuwa gidan mahaifiyar ta a cikin wata motar haya ‘da jini a hannun ta,’ a cewar Patricia, ‘yar uwar wadda ake zargin. Surukar shi ta gano gawar mijinta akan gado a gidan da yake zaune tare da matar shi da yaron shi dan shekara biyar.

Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa, ya samu raunuka daban-daban a jikin shi, ciki har da kirjin shi, kuma an yi mai yankan rago. An kwantar da Amado Cattaneo a sashin kula da masu tabin hankali na cibiyar kula da lafiya ta La Plata, inda za a yi mata bincike.

Advertisement