Al'umma

Wata Mata Ta Bayyana Yanda Dan Fashi Ya Shiga Gidan Ta, Kuma Ya Fita Da Ita A Tsirara

Wata mata ta bayyana yadda wani dan fashi da makami ya shiga gidanta da ke Apete, Ibadan.

Ta bayyana cewa dan fashin shi kadai ya cire dukkan fitulun tsaro da ke kusa da gidanta sannan ya yaga ragar kowane tagar gidan sannan ya shiga ciki.

Ganin ita kaɗai a gidan yasa ta cire sandunan rodi biyu na kofar gidan inda ɗan fashin ya samu damar shiga gidan har ɗakin ta kafin ya tadda ta da mari.

Koda ɗan fashin ya shigo tana tsirara kuma a hakan ya fito da ita daga gidan.

Don ko zai tausayawa mata tace masa tana da ciki amma sai ya amsa da cewa abokansa suna neman mace mai ciki da za su yi amfani da ita wajen tsafi.

A wannan lokacin tace ba ta da wani zabi illa ta afka masa don ta tsira.

Ta samu raunuka yayin da take fafatawa dan shi kadai. Alhamdu lillahi ta tsira da ranta.

Advertisement