Laifuku

Wata Mata Ƴar Shekara 18 Ta Jefa Ɗan Tsohon Mijin Ta Rijiya, Kuma Ya Mutu

Jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina sun kama wata Maryam Habibu a ranar Juma’a.

An zargi yarinyar mai shekaru 18 da jefa dan tsohon mijin ta mai suna Jamilu Rabi’u mai shekaru hudu a cikin rijiya.

Matakin da matar da ‘yar asalin kauyen Leko da ke karamar hukumar Danja ta jihar Katsina ta dauka, ya kai ga mutuwar dan tsohon mijin na ta.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, yace wadda ake zargin ta je gidan tsohon mijin ta ne ta lallaba yaron zuwa wani wuri da ke kusa, ta jefa shi cikin rijiyar, ta kashe shi.

Maryam yayin da take zantawa da manema labarai ta ce tun da farko ta yi amfani da fartanya kan matar tsohon mijin ta ta farko, kuma har yanzu shari’ar tana nan a kotu.

Wadda ake zargin ta ce ta taba kona katifar da mijin ta ya siyo ma wata matar shi, saboda ya kasa saya mata ita ma.

Advertisement