Al'umma

Wata budurwa da ta bace bayan ta hau motar BRT ‘an ga gawar ta babu sauran sassan jiki’

Oluwabamise Toyosi Ayanwole, budurwa yar shekara 22 da ta dauki hoton kanta a cikin wata motar safa ta BRT a Legas bayan ta yi shakkun motsin direban, an same ta a matatta.

Bamise ta hau motar bas ta BRT mai lamba 240257 daga tashar motar Chevron, Lekki, ta nufi Oshodi da misalin karfe 7 na dare. ranar Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022, akan hanyar ta ta gida daga wurin aiki.

A cikin tafiya sai ta ji ba dadi don ita kadai ce a cikin bas din da duhu sai ta fara daukar bidiyo.

Advertisement

A cikin faifan bidiyon ta nemi a yi mata addu’a domin hankalin ta bai kwanta ba. Ta bayyana cewa direban bai dauko kowa ba bayan ya dauke ta.

Bata sake komawa gida ba kuma wannan shine na karshe da masoyan ta suka ji daga gare ta.

Lokacin da bata dawo gida ba yan uwan ta suka shiga neman motar BRT da ta dauki hoton a ciki, suna amfani da lambar rajistar motar.

Da take mayar da martani, rundunar yan sandan ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da alaka da bacewar Bamise.

Advertisement