Lafiya

Wata ƙungiya ta roki Buhari da ya saki fasfot din El-Zakzaky da matar shi

Wata kungiya mai suna Advocate for Social Justice, ta roki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta dawo da takardun tafiye-tafiye na jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky da na matarsa ​​Malama Zeenatuddin Ibrahim bisa dalilai na jin kai.

Kungiyar ta shaidawa gwamnati cewa ma’auratan na bukatar takardun balaguron tafiya don cigaba da jinya a kasashen waje sakamakon matsalolin da suka fuskanta a gidan yari.

Kungiyar ta bayyana cewa babbar kotun jihar Kaduna ta sallame su tare da wanke su daga tuhumar da ake musu.

Advertisement

Sakataren yada labaranta, Mista Segun Fanimo, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce hatta shugaban kasa Muhammadu Buhari yakan dauki hutu daga bakin aikinsa domin kula da yanayin lafiyarsa a wajen Najeriya.

“Don haka babu wata hujjar hana shugaban ‘yan Shi’a ‘yancin zuwa kowace kasa don kula da yanayin rashin lafiyarsa.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Kamar yadda kuka sani, sama da watanni shida ke nan da babbar kotun jihar Kaduna ta wanke jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibraheem Zakzaky tare da matarsa, bayan shafe kusan shekaru shida a tsare ba bisa ka’ida ba.

Advertisement