Al'umma

Wata Ƙungiya Ta Buƙaci Gwamnonin Kudu Maso Gabas Da Su Kori Almajirai Daga Yankin

Wata kungiya mai suna Ohanaeze Youth Council, ta yi kira ga gwamnonin jihohin Kudu maso Gabashin Najeriya da su kori dukkan almajirai a yankunan su.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Okechukwu Isigusoro, da Sakatare-Janar, Nnabuike Okwu, kungiyar ta ce ya kamata a kuma binciki yadda kwamitin yaki da cutar COVID-19 na Enugu ya kama kananan yara daga Kano.

Sanarwar ta cigaba da cewa, “Mu Majalisar Matasa ta Ohanaeze, mun bayyana kama Almajiran Kano a kan iyakar Enugu da Hukumar kula da cutar COVID-19 ta Jihar Enugu ta yi a matsayin ayyukan ‘yan damfara da kuma munanan ayyuka na dattawan Arewa don fitar da almajirai masu dauke da cutar Coronavirus zuwa Kudu maso Gabas.

Advertisement

“Majalisar matasan Ohanaeze ta yi kira ga gwamnonin Kudu-maso-Gabas da su duba halin da suke ciki dangane da hukuncin da gwamnonin Arewa suka dauka na haramta almajiranci daga duk inda aka same su zuwa jihohin su na asali, sannan su dauki matakin tabbatar da cewa dukkan almajirai da ke kan tituna na Kudu-maso-Gabas ana mayar da su ne bisa tsarin da gwamnonin Arewa suka kafa.”

Advertisement