Al'umma

Wasu yara maza 2 yan shekara 6 da 8 sun nutse cikin ruwa wajen ciro takalmi

Wasu yara maza biyu masu suna Michael Nyam mai shekaru 8 da kuma Elijah Solomon mai shekaru 6 sun nutse a dam din da ke Rayfield Resort da ke Jos a jihar Filato.

Wani shaidar gani da ido, Mista Gyang Pwol, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Jos cewa yaran sun nutse ne da yammacin ranar Asabar, 19 ga Fabrairu.

Pwol ya bayyana cewa mutanen biyu sun nutse ne a lokacin da suke kokarin dawo da takalmin daya daga cikin abokansu da ya fada cikin dam din.

Advertisement

“Sun yi tsalle cikin zurfin ruwa a cikin dam don ceto wani takalmin abokin su, abin takaici, yawan ruwan ya yi yawa. Kafin taimako ya zo, sun nutse,” inji shi.

Pwol, wanda kuma ya tabbatar da cewa an binne gawarwakinsu, bai yi karin bayani ba.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Ogaba, ya ce ba a kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda ba.

Advertisement