Labarai

Wasu Yan Daudu Sun Farfasa Ofishin Hisbah A Kano Bayan Murabus Ɗin Daurawa

Mun samu wasu rahotonnin ke cewa wasu da ake zargin cewa yan Daudu ne sun farwa wani ofishin hukumar a jihar Kano jim kaɗan bayan saukar kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wasu tawagar ƴan Daudu a Rijiyar Lemo, Kwanar Jajira sun fara farfashe a ofishin Hizba ɗin dake Yankin.

idan za’a iya tunawa, 1 ga watan Machi, 2024 Sheikh Daurawa ya sanar da sauka daga shugabancin Hisbah bayan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya soke yadda hukumar ke aikinta.

Kalaman gwamnan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Hisbah ta kame wasu yan TikTok mata biyu da ake zargi da yaɗa kayayyakin batsa da maɗigo, Ramlat Princess da Murja Kunya da shafukan sada zumunta.

Majiya – ALFIJIR HAUSA

Advertisement