Al'umma

Wasu samari sun yanka budurwa, sun kona kan ta don yin tsafin kuɗi a Ogun

An samu tashin hankali a yankin Oke Aregba dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, bayan da aka kama wasu samari maza suna kona kan wata yarinya da aka ce suna da alaka da daya daga cikinsu, domin yin tsafin kudi.

Da sanyin safiyar ranar Asabar, wani Mista Segun Adewusi, wanda shine jami’in tsaron al’umma, ya lura cewa wasu yara maza hudu suna kona wani abu da ake zargin kan mutum ne a wata tukunyar da ke kan hanya.

DAILY POST ta habarto cewa, nan take mai gadin ya sanar da ‘yan sanda a ofishin Adanan, inda suka je wurin da lamarin ya faru domin cafke uku daga cikin yaran yayin da daya ya gudu kafin ‘yan sanda su iso.

Advertisement

Wata majiya da ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, ta ce yarinyar da aka kashe mai suna Rofiat, mazauniyar Idi-Ape ce; ta kasance budurwa ga wani Soliu, wanda yanzu ke cikin hannun gidan ‘yan sanda.

An ce Soliu ya yaudari yarinyar zuwa dakinsa, inda ya rike ta ya bukaci daya daga cikin abokansa ya yanka ta da wuka.

Wadanda ake zargin sun hada da Wariz Oladeinde mai shekaru 17 daga Kugba da Abdulgafar Lukman mai shekaru 19 daga Kugba da Mustakeem Balogun daga Bode Olude duk a Abeokuta. Soliu shine saurayin yarinyar, ya gudu, amma daga baya aka kama shi.

“Sun kashe Rofiat, suka yanke mata kai, suka tattara gawar mara kai a cikin buhu sannan suka fara kona kan a tukunya. Sun gaya wa ’yan sanda a gaban taron jama’a cewa suna so su yi amfani da shi wajen ibadar kuɗi.

“’Yan sanda sun tafi da gawar zuwa dakin ajiyar gawa,” wata majiya ta shaida wa wakilinmu ranar Asabar.

Advertisement