Tsaro

Wasu da ake zargin Fulani ne sun kashe masu zaman makoi 3 a Benue

Wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne sun kashe wasu makoki uku a karamar hukumar Guma da ke jihar Benue.

Advertisement

An ce makiyayan sun yi kwanton bauna ne a kan hanyar Iordye-Gbanjimba da misalin karfe 5 na yammacin ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, inda suka harbe wadanda aka kashen, maza biyu da mace daya, wadanda suke kan babura a lokacin da suke dawowa daga jana’iza.

Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 48 bayan da wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe mutane biyar a karamar hukumar Gwer West da ke jihar.

Advertisement

Biyu sun mutu nan take sakamakon raunukan harbin bindiga yayin da dayan kuma aka yi masa yankan rago har lahira.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Nathaniel Ikyur, ya ce sojojin da ke aiki da rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ sun kwato gawarwakin tare da ajiye gawarwakin a babban asibitin Gbajimba.

“Abin takaici, wannan shi ne halin da ‘yan asalin jihar Benuwe ke ciki a hannun Fulani makiyaya da suka mamaye jihar da nufin kwace filayen kakanninmu. Ya kara da cewa.

Advertisement