Tsaro

Wasu Ƴan Matan Chibok Sun Bayyana Yadda Suka Samu Hanyar Tsira Daga Ƴan Boko Haram

A wani labarin da jaridar Vanguard ta wallafa a yanar gizo da yammacin yau, ta bayyana cewa 13 daga cikin ‘yan matan Chibok da aka ceto ko kuma suka tsira, wadanda a halin yanzu su zama uwaye, sun roki gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Borno da su dawo da su makaranta kamar yadda suka yiwa abokan su, wadanda suka tsira a gaban su.

Bayanin da aka bayar ya bayyana cewa hakan ya zo ne a jiya, yayin da manema labarai ke zantawa da wasu ‘yan matan a sansanin su da ke Borno.

Yayin da suke zantawa da wakilin jaridar Vanguard, uku daga cikin ‘yan matan Chibok da suka hada da Ruth Ngalada, Maryam Dauda da Hassana Adamu, sun bayyana yadda suka kubuta daga hannun wadanda suka sace su.

Advertisement

Daya daga cikin su ta ce, “Mun samu nasarar tserewa ne bayan da wasu ‘yan Boko-Haram suka nuna mana hanya.

Wata wacce abin ya rutsa da ita yayin da ta bayyana yadda ta kubuta ta ce, sun yi kamar za su ziyarci abokan aikin su ne ko kuma daliban makarantar da ke kauyen na gaba, inda suka yi amfani da damar da suka samu suka tsere cikin daji kafin mutanen kauyen su ceto su.

Advertisement