Laifuku

Wani Mutum Ya Yiwa Wata Mata Fyade A Gaban Yar Ta

Rundunar jami’ai ta NSCDC reshen jihar Kwara ta kama wani mutum mai shekaru 47 bisa zargin yi wa wata mata fyade a gaban ‘yar ta ‘yar shekara biyu.

Advertisement

A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar (PRO) Olasunkanmi Ayeni ya fitar, ta ce an aikata laifin ne a ranar sabuwar shekara a unguwar Oloje da ke Ilorin, babban birnin jihar.

Sanarwar ta kuma ce wanda ake zargin Ganiyu Yusuf ya tafi da kwamfutar tafi-da-gidan ka guda biyu da wayoyin android guda biyu na wadda abin ya shafa bayan da ya aikata wannan danyen aikin.

Advertisement

“An samu rahoton aikata laifin fashi da fyade a hedkwatar hukumar NSCDC ta jihar Kwara, Ilorin a ranar 1 ga Janairu, 2022.

“Rundunar ta fara bincike sosai kan wanda ake zargin bayan an samu rahoton faruwar lamarin. An yi sa’a, an gano wanda ake zargin a Mokwa, jihar Neja a ranar 5 ga Janairu, 2023.

“Wanda ake zargin, Ganiyu Yusuf, mai shekaru 47, kuma dan asalin Abeokuta, jihar Ogun ya amsa cewa ya kutsa gidan ne a wannan rana ta cikin rufin asiri. Bayan samun shiga gidan da ke unguwar Oloje a Ilorin, ya yi galaba a kan matar da ke ita kadai da jaririyar ta yar shekara biyu a gidan.

“Ya yiwa matar fyade a gaban ‘yar ta ‘yar shekara biyu sannan ya tafi da kwamfutar tafi-da-gidan ka biyu da wayoyin android guda biyu na wadda abin ya shafa.

“Hukumar tana ci gaba da neman masu sayen kayayyakin na shaida.

“Kwamandan hukumar na jiha, Mallam Muhammed Tukur Ibrahim, yana kira ga jama’a da su lura da abin da suke saya a kowane lokaci.

Sanarwar ta ce “Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu domin gurfanar da shi nan take”.

Advertisement