Alaƙa

Wani Mutum Ya Tayar Da Kura Bayan Ya Ce Duk Wanda Ya Yiwa Matar Shi Ciki Ya Aika Zunubi

Wani mai wa’azin Kirista ya fuskanci turjiya daga masu sauraron shi sa’ad da ya ce duk mutumin da ya yiwa matar shi ciki ya aikata zunubi.

Advertisement

Mai wa’azin yana wurin shiga mota na bas ne yana wa matafiya wa’azi lokacin da ya yi wannan furucin.

Sai aka ce ya maimaita abin da ya fada, sai ya sake, yana mai cewa: “Idan mutum ya yi wa matar shi ciki, mutumin ya yi zunubi.

Advertisement

Ya kara da cewa: “Zunubi ne domin abu ne na duniya.”

Fasinjoji suka ce mai kenan bai kamata a haife shi a wannan yanayin ba, sai ya amsa da cewa, “Shin na ce wani ya haife ni, na ce wani ya haife ni?”

Daga karshe ana kyautata zaton cewa wannan mutumin yana matsala wacce aka danganta da rashin na hankali ko kuma da gangan yake yi.

Advertisement