Al'umma

Wani mutum ya saki matar shi bayan ƴan bindigar da suka sace ta sun sako ta

Tsohon Sanatan da ke wakiltar mutanen Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya bayyana yadda wani mutum dan garin Zariya ya saki matar shi, bayan da wasu yan bindigar da suka sace ta suka sako ta.

A wani sako da ya wallafa a shafin shi na Twitter, Shehu Sani ya bayyana cewa sun shafe shekara 20 da aure, amma mutumin ya yanke shawarar rabuwa da ita bayan wasu yan bindiga da suka yi garkuwa da ita da wasu mutane suka sako ta.

Da yake karin haske, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa mutumin ya sake ta ne saboda yana zargin yan fashi sun kwana da ita. Daga karshe ya yi kira ga malaman addini da su sa baki a kan wannan batu.

Advertisement

Wannan hakika mai tsanani ne. Ni kuwa ban ga dalilin da zai sa mutumin nan ya saki matar shi ba, don kawai an sace ta, don ba laifin ta ba ne. Kamar yadda Shehu Sani yace malaman addini su yi abin da ya kamata, ta hanyar nasiha ga wannan mutum, domin ya karbi matar shi.

Advertisement