Al'umma

Wani mutum ya cakawa mahaifiyar shi wuƙa ta mutu lokacin da yake faɗa da matar shi

A kwanakin baya ne aka kama wani mutum bayan da ya kashe mahaifiyar shi bisa kuskure a Zawiyya Tudunwada Kontagora, jihar Neja.

An ruwaito cewa yana fada da matar shi ne mahaifiyar shi ta shiga tsakani. Daga nan sai mijin ya kai wa matar shi hari, kuma yayi yunkurin dabawa matar shi wuƙa, amma ana cikin haka sai yayi kuskure ya dabawa mahaifiyar shi dake kokarin raba faɗan.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama mijin nan take bayan labarin rasuwar mahaifiyar shi ya bazu.

Advertisement
Advertisement