Labarai

Wani Makashin Matashi Ya Sheƙe Mata 42 Har Lahira A Asirce A Kenya

Wani dan kasar Kenya da ake zargi da kasancewa “mai kisan kai” ya bayyana a gaban wata kotu a Nairobi, babban birnin kasar a wannan makon bayan ‘yan sanda sun tuhume shi da laifin kisan kai bayan gano gawarwakin mutane tara da aka yi.

‘Yan sanda sun kama Collins Jumaisi Khalusha, mai shekaru 33 a safiyar ranar Litinin, inda aka gurfanar da shi a gaban kuliya a washe gari, tare da alakanta shi da gawarwakin da aka gano warwatse a cikin wani wurin zuba shara a unguwar marasa galihu a Nairobi ranar Juma’a.

Khalusha, in ji jami’ai, ya amsa laifinsa. ya kashe mata 42, tare da zargin wacce ya fara kashewa ta farko matarsa ​​ce.

Daraktan binciken ‘yan sandan Kenya Mohamed Amin ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin cewa, “Muna fama da wani mai kisan kai, mai kisan kai na rashin imani wanda ba ya mutunta ran dan Adam, wanda ba shi da mutuntawa da darajantawa.

Sai dai lauyan wanda ake zargin, John Maina Ndegwa, ya fada a gaban kotu a ranar Talata cewa an azabtar da Khalusha wanda hakan yasa shi yin wannan furucin. Masu gabatar da kara sun musanta wadannan zarge-zarge.

Advertisement