Tsaro

Wani Jirgin Yaki Da Ba’a San Daga Inda Yake Ba, Ya Sakar Wa Yan Sa-Kai Bam Lokacin Da Suke Shirin Kai Wa Yan Bindiga Hari

A cewar wani rahoto da jaridar Vanguard ta wallafa, wani jirgin da ba a san ko wane ne ba ya kai wani samame a yankin Galadima Kogo da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja a ranar Talata, 24 ga watan Janairu, 2023.

An kashe ‘yan banga da dama wadanda rahotanni suka ce suna kare kauyen daga harin ‘yan bindiga, yayin harin ta sama. An bayyana cewa kwamandan kungiyar ‘yan banga da wasu mambobi da dama sun samu munanan raunuka a harin.

A cikin rahoton, an ce ’yan banga sun hada kai don kai farmaki kan ‘yan bindigar da suka kai farmaki kauyen tun da farko suka yi awon gaba da wasu mazauna kauyen, a lokacin da jirgin ya taho daga ko’ina, suka fara luguden wuta a inda suke.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa kwamishinan tsaron cikin gida da jin kai na jihar Neja, Emmanuel Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin. Sai dai ya kasa bayyana adadin wadanda suka mutu da kuma inda jirgin ya fito.

Daya daga cikin shugabannin al’ummar da ya zanta da Vanguard News a boye, ya bayyana cewa sun yi amfani da motocin kirar Hilux guda biyu wajen kwashe ‘yan banga da suka mutu bayan harin. Ya ce: “Wannan ci gaban abu ne da ba za a iya yarda da shi ba, kamar yadda a yanzu, ba zan iya cewa adadin mutanen da aka kashe ba, amma na san suna da yawa.”

“Abin da na sani shi ne, motocin kirar Hilux guda biyu sun kwashe matattu daga sansanin. ‘Yan banga ne suke ba mu kariya daga wadannan ‘yan ta’adda, kuma yanzu da aka kashe da yawa daga cikinsu, muna hannun ‘yan bindigar,” inji majiyar.

Advertisement