Al'umma

Wani dan sanda ya kashe wani yaro akan ya sha ruwan pure na ₦20 a Kogi

A yanzu haka ana zanga-zanga a yankin Kabba da ke jihar Kogi, a ranar Asabar, bayan wani matashi da wani dan sanda da ba a tantance ba ya kashe shi kan kudin ruwan pure water ₦20.

Rahotanni sun bayyana cewa, mutuwar yaron ya haifar da hargitsi a garin Kabba daga fusatattun matasa a yankin.

An kuma bayyana cewa, masu zanga-zangar sun yiwa ofishin ‘yan sanda kawanya a Kabba, inda suke rera wakokin yaki, yayin da jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa jama’a.

Advertisement

Jaridar Blueprint ta tattaro cewa yaron yana shan ruwan pure water na dan sandan ne lokacin da aka kashe shi.

Kwamishinan yan sandan jihar Kogi, Edward Egbuka ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Egbuka yace dan sandan da ake zargin ya yi kokarin kare kansa ne kawai bayan an yi rikici da wanda abin ya shafa, kamar yadda wani rahoto na farko ya nuna.

Advertisement