Al'umma

Wani dalibi na makarantar su Hanifa Abubakar ya ɓace sama da shekara daya

Shugaban makarantar Noble Kids Academy da ke Kano ya kasance babban abin tattaunawa a baya-bayan nan bayan da rundunar yan sandan jihar Kano ta kama shi da laifin yin garkuwa da ta, da sanya guba da kuma kashe dalibarsa yar shekara 5 mai suna Hanifa Abubakar.

Advertisement

Yayi hakan ne bayan ya bukaci a ba shi kudi naira miliyan 6,000,000 kuma ya karbi ₦3,000,000 daga hannun iyayenta kafin a kashe ta.

Kasa da kwanaki uku da gano rasuwar Hanifa, wata mata mai suna Fauziyya D Sulaiman ta bayyana cewa wani yaro dan shekara 11 mai suna Yusuf wanda kuma dalibin makaranta daya da Hanifa an sanar da batar shi sama da shekara guda da ta gabata, jaridar Daily Nigerian. babban editan Jaafar Jaafar ne ya bayyana hakan a shafin Facebook.

Advertisement

Yaron da aka ce yana zaune a unguwar makarantar ya bace har ya zuwa yanzu kuma ya bace bayan ya tafi makarantar da yammaci.

Yanzu haka dai shugaban makarantar Noble Kids Academy zai samu karin tambayoyin da zai amsa domin iyayen Yusuf sun mika kokensu ga hukumar da ta dace, Fauziyya ta bayyana.

Advertisement