Al'umma

Wani Attajirin dan kasar Japan ya bada gudummawar dala miliyan $8.7 ga Ukraine

Wani hamshakin attajiri dan kasar Japan, Hiroshi “Mickey” Mikitani, a yau Lahadi, yayi alkawarin bayar da gudummawar dalar Amurka miliyan $8.7 ga gwamnatin Ukraine, biyo bayan mamayar kasar da Rasha ta yi a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mikitani, wanda ya kafa kuma Babban Jami’in Gudanarwa (Shugaba) na giant e-commerce, Rakuten, wanda ya kira mamayewar Rasha “kalubale ga dimokiradiyya,” yace a cikin wata wasika da aka aikawa shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, cewa “gudummawar ¥1 biliyan ($ 8.7 miliyan) zai tafi zuwa ayyukan jin kai don taimakawa mutanen Ukraine da ke fama da tashin hankali.”

“Tunanina yana tare da ku da kuma mutanen Ukraine,” Mikitani, wanda yace ya sadu da Zelensky lokacin da ya ziyarci Kyiv a 2019, ya rubuta a cikin wasikar shi.

Advertisement

“Na yi imani cewa tattake yancin kai na Ukraine cikin lumana da dimokuradiyya ta hanyar da ba ta dace ba kalubale ne ga demokradiyya.

Advertisement