Al'umma

Wani ɗan kasar Tanzania ya gina wa kan shi kabarin miliyan ₦1,700,000 tun kafin ya mutu

Wani mutum dan kasar Tanzania ya tayar da hankalin mutanen kauyensu saboda ya gina kabarin da za a binne shi idan ya mutu.

Advertisement

Patrick Kimaro, mai shekara 59, ya ce sannu a hankali iyalai da danginsa sun fara hakuri tare da yarda da matakin nasa, wanda mutanen garin ke kallo a matsayin alamar wani mummunan abu.

Shugabannin gargajiya daga kabilar Mista Kimaro, a yankin Kilimanjaro, sun ce bai kamata a gina ƙabari ba, bisa jiran mutuwa, kuma bai kamata ƙabari ya kasance ba komai a cikinsa tsawon lokaci.

Advertisement

Mista Kimaro, wanda ɗan sanda ne ya shaida wa BBC Swahili cewa tun a watan Janairu ya fara gina ƙabarinsa domin rage wa iyalansa ɗawainiyar jana’izarsa idan ya mutu.

Ya ce kasancewarsa haihuwar fari a wajen iyayensa ya san irin ɗawainiyar da ya sha wajen binne iyayen nasa waɗanda suka mutu wata shida a tsakaninsu, saboda haka ne ya ce ya yanke shawarar gina ƙabarin nasa domin kada ‘ya’yansa su sha irin wahalar da ya shiga.

Mista Kimaro zai ware wasu kuɗaɗe domin sayen akwatin gawarsa, kuma yana ganin sauran kuɗaɗen da za a buƙata wajen ɗawainiyar jana’izarsa idan ya mutu iyalan za su iya samarwa.

Haka kuma yana shirin yi wa kabarin nasa inshora ko da za a samu matsala irin ta ambaliyar ruwa da za ta iya lalata shi.

Kudin da ya kashe wajen gina ƙabarin da kawata cikinsa sun kai dala dubu uku, kusan sama da naira miliyan daya da 700,000.

Sai dai wasu daga cikin iyalinsa tuni su har sun fara sabawa da kabarin inda suke zama a kusa da shi suna hira. Mai gadin gidan Mista Kimaro ya ce wasu makƙwabtansu sun daina zuwa gidan tun bayan da ya gina ƙabarin.

Advertisement