Addini

Wanda ya zo na ɗaya a gasar ‘Kiran Sallah’ zai kashe kyautar kuɗi fiye da miliyan ₦220 a Saudiyya

Kamar yadda yanar gizo ta makkahnewspaper.com ta wallafa a shafin ta makaranta Alkur’ani sama da 79,999 da suka fito fiye da 79 daga sassan duniya daban daban ne ke fafatawa a gasar wacce ke gudana a kasar Saudiyya.

Gasar an ware mata kyautar tsabar kudi har dalar Amurka miliyan $3.2, da za’a lashe a matakai daban daban.

Wanda ya zo na daya da mafi kyawun murya a karatun kur’ani mai tsarki ya samu dala miliyan $1.3, kimanin miliyan (Ɗari biyar da arba’in da dubu ɗari takwas) ₦540,800,000, yayin da wanda ya zo na daya a wajen gabatar da kiran sallah ya samu dala $533,000, kimanin miliyan (Ɗari biyu da ashirin da ɗaya da dubu ɗari bakwai da ashirin da takwas) ₦221,728,00.

Ragowar kudaden kyaututtukan an raba su ne tsakanin wasu yan takara shida na baya.

Back to top button