Labarai

WAEC Ta Sakin Sakamakon Jarabawar Kammala Sakandire Ta 2024

A ranar Litinin ne Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma (WAEC) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma na shekarar 2024 ga ‘yan makaranta.

WAEC ta tabbatar da hakan a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na X.

Ya sanar da daliban da suka yi jarrabawar da su shiga waecdirect.org don samun sakamakon su.

“Muna farin cikin sanar da dalibai da suka zauna WASSCE ta 2024, cewa an fitar da sakamakon a hukumance a yau Litinin, 12 ga Agusta, 2024.

“Don samun damar sakamakon, shiga waecdirect.org.”