Al'umma

Wa Zai Kwatanta Shehu Shagari A Matsayin Ɗan Ta’adda Don Fulani Na Kashe Mutane – Dogara

Yakubu Dogara, tsohon kakakin majalisar wakilai ya mayar da martani keɓancewar kabilanci da ake yiwa Fulani a matsayin ‘yan ta’adda inda ya bayyana cewa ba daidai ba ne na nuna kabilanci.

Dogara ya kara da cewa Fulani sun kafa gwamnati mai kyau a Najeriya a baya inda ya lissafo wasu da dama da suka rage a tarihin al’umma.

Yace, ”Na ji mutane na ce mini babu yadda za a yi in goyi bayan Bafulatani saboda Fulani na kashe mutane. Amma ka ga wani lokaci mukan manta da tarihi cikin sauki.

Advertisement

Mun taba samun shugaban kasa Shehu Shagari a baya, wa zai taba kwatanta Shehu Shagari a matsayin dan ta’adda saboda Fulani suna kashe mutane?

Mun samu shugaba Umaru Musa ‘Yar’aduwa wanda shi ma Bafulatani ne, shi kuma mutumin yana laushin hali.”

Advertisement