Tsaro

Uzodinma ya zo ya halaka Imo ne, ba shi da ƙarfin jagorantar jihar – Okorocha

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, yace manufofin Hope Uzodinma a jihar shine kashe-kashe da ruguzawa, kuma ba shi da karfin iko da abin da ya kamata ya yi na mulkin jihar a tsarin dimokuradiyya.

Okorocha, wanda yanzu shine Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma a majalisar dattijai ta kasa, a wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Sam Onwuemeodo ya fitar, yace “gwamnatin dake yanzu a jihar karya ce ta abin da ya kamata gwamnatin jiha ta kasance.”

A cikin sanarwar da ya rabawa Ripples Nigeria a ranar Asabar, Okorocha ya zargi Uzodinma da jefa Imo cikin wani yanayi na rashin gaskiya da rashin tsaro inda kashe-kashe da sace-sacen mutane suka zama ruwan dare.

Advertisement
Advertisement