Kasuwanci

Uku da ransu, bakwai sun bace bayan fashewar jirgin dakon mai a Najeriya

An gano wasu ma’aikatan jirgin guda uku da ke cikin wani jirgin ruwan dakin mai da ya fashe a makon da ya gabata a gabar tekun Najeriya, yayin da wasu bakwai suka bace, kamar yadda ma’aikacin jirgin ya bayyana.

Ikemefuna Okafor, babban jami’in Shebah Exploration & Production Company Ltd (SEPOL), yace a yammacin ranar Lahadi kamfanin zai tabbatar da cewa wadanda suka tsira sun samu kulawar da ta dace.

Okafor ya kara da cewa “an gano gawar mutum daya a kusa da wurin”, amma ba a bayyana ko na wani ma’aikacin jirgin ne ba.

“Har yanzu ba a gano asalin gawar ba,” in ji Okafor. Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin gano sauran ma’aikatan jirgin, “tsaftace da takaita lalacewar muhalli, da kuma gano musabbabin fashewar”.

Back to top button