Tsaro

Ukraine: Macron, Putin sun amince su yi aiki don tsagaita wuta

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Rasha Vladimir Putin sun amince da yin aiki don tsagaita wuta a gabashin Ukraine, inda ministocin harkokin wajen kasashen biyu za su gana a cikin kwanaki masu zuwa.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a shirye yake ya gana da Putin don gano “abin da shugaban Rasha ke so” da kuma neman “kwanciyar hankali” a yayin da ake kara nuna damuwa kan yiwuwar mamayewa.

Tashe-tashen hankula a gabashin Ukraine sun yi kamari a ‘yan kwanakin nan. An dai shafe shekaru ana gwabza fada a tsakanin sojojin Ukraine da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rasha, amma hare-haren bama-bamai na baya-bayan nan na iya haifar da yakin basasa.

Advertisement
Advertisement