Wasanni

UEFA ta mayar da wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai daga Rasha zuwa Faransa

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai (UEFA) a ranar Juma’a ta sanar da sauya wurin da za’a buga wasan karshe na gasar zakarun Turai ta 2022 daga kasar Rasha.

UEFA ta mayar da wasan karshe na gasar zakarun Turai daga Rasha zuwa Faransa.

Hukumar ta dauki matakin ne a taron gaggawa na ranar Juma’a.

Advertisement

UEFA ta ce wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai wanda aka shirya gudanarwa a Gazprom Arena a St Petersburg a ranar 28 ga Mayu zai gudana ne a filin wasa na Stade de France da ke Saint-Denis, Paris.

Sanarwar da hukumar kwallon kafar Turai ta fitar ta ce an dauki matakin ne saboda mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.

Sanarwar ta ce: “Hukumar zartaswa ta UEFA a yau ta gudanar da wani taro na ban mamaki biyo bayan ta’azzara matsalar tsaro a Turai.

“Kwamitin zartaswa na UEFA ya yanke shawarar mayar da wasan karshe na 2021/22 UEFA Champions League Men’s Champions League daga Saint Petersburg zuwa Stade de France a Saint-Denis. Za a buga wasan kamar yadda aka tsara tun a ranar Asabar 28 ga Mayu da karfe 21:00 na CET.”

Advertisement