Tsaro

Turkiyya a shirye take ta taimaka wajen warware rikicin Ukraine – Inji Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi tayin karbar bakuncin shugabannin Ukraine da Rasha yayin da Ankara ke cigaba da yunkurin sasanta rikicin.

Da yake jawabi ga manema labarai a birnin Kyiv a ranar Alhamis din da ta gabata bayan ya tattauna da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelenskyy, Erdogan ya ce a shirye yake ya shirya tattaunawar zaman lafiya a cikin fargabar da kasashen yammacin duniya ke yi na cewa Rasha na shirin mamaye makwabciyarta.

Turkiyya a shirye take ta bada nata nata gudunmuwar domin warware rikicin da ke tsakanin kasashen abokantaka biyu da suke makwabtaka da su a tekun Black Sea. Na sake fada yayin tattaunawa cewa za mu iya yin farin ciki da karbar bakuncin babban taro a matakin shugabanni, ko kuma mu dauki nauyin tattaunawa a matakin fasaha,” inji shi.

Advertisement

Mahukuntan yammacin duniya na fargabar kutsawar Rasha ta kusa ganin yadda Moscow ta yi tarin sojoji sama da 100,000 a kusa da kan iyaka da Ukraine, amma fadar Kremlin ta musanta cewa tana da shirin kai hari.

Advertisement