Labarai

Turka-Turkar Emiefele Da DSS: Ba Mu Dirar Wa Hedkwatar CBN Ba – DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a ranar Litinin ta karyata labarin da ke cewa jami’an ta sun mamaye ofishin gwamnan babban bankin Najeriya Mista Godwin Emefiele tare da kama shi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dr Peter Afunanya ya rabawa manema labarai, hukumar ta bayyana mamayewar da kuma kame gwamnan babban bankin na CBN a matsayin, “labari na karya da yaudara.”

Sanarwar ta ce, “hankalin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya kai kan labarin karya da ake yadawa cewa jami’an ta sun mamaye babban bankin Najeriya tare da kama gwamnan shi, a yau 16/1/23. Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce.

Advertisement

Wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta rawaito cewa “Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya, DAS, sun mamaye hedikwatar babban bankin Najeriya, CBN, inda suka mamaye ofishin gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele.

A cewar shi, “Da isar su hedikwatar CBN a ranar Litinin da rana, jami’an DSS sun shigo da motoci kusan 20 dauke da makamai.

“Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Mista Emefiele.”

Ya kara da cewa an yi taho-mu-gama tsakanin hukumar da Mista Emefiele kan zargin bada kudaden ta’addanci.

A cewar ta, tun da farko hukumar leken asirin ta nemi kotu ta kama Mista Emefiele amma ya tafi kasar domin hutun shekara.

Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta hana hukumar DSS kama, gayyata, ko kuma tsare Mista Emefiele.

Source: Tribune

http://opr.news/10f1204230116en_ng?link=1&client=news

Advertisement