Tsohon Shugaban Jam’iyyar Shi’a A India Ya Shigar Da Kara A Gaban Babban Kotun Domin Neman A Cire Ayoyi 26 Daga Cikin Al’qur’ani

, , Leave a comment

Tsohon shugaba jam’iyyar shi’a a kasar India mai suna Waseem Rizvi, wadda ake kira (Central Board of Waqf , Trust), a yankin Uttar Pradesh, ya shigar da kara a gaban wata babbar kotu dake a kasar ta India domin neman a cire wasu wasu ayoyi dake cikin Al’qur’ani maigirma guda 26, wadand ya kira ayoyin tashin tashin hankali, (Wa’iyazubillah).

Karanta: BA ZA MU SAKE YARDA WANI A KOWACE JIHA YA SAKE ZAGIN SAHABBAI BA-SHEIKH BALA LAU

READ ALSO:  Hukumomi A Najeriya Sun Saki Mayakan Boko Haram 1,0000 Daga Magarkama A Asirce

Waseem, wanda mai shirya fina-finai ne a India, ko a kwanakin baya ma ya shigar da wata kara a kotu inda yayi korafin cewa wani sashe daga cikin Al’qur’ani maigirma yana kawo tada zaune tsaye, sannan yace yana ingiza mutane domin yin ta’addanci.

Waseem Rizvi

Wadansu masu zanga-zanga a babban birnin Bangladesh, Dhaka, yan jam’iyyar (Jamaat-e-Islami) mai yawan musulmi sun nemi gwamnatin kasar India da ta gurfanar da Waseem a gaban shari’a saboda yunkurin batawa musulmin duniya suna da yayi da sunan addini.

READ ALSO:  Barayin Sunyi Yunkurin Kaiwa Gidan Salame Hari A Sakkwato

[Ainahin Labari: Jihad Watch.