Siyasa

Tsohon ministan wasanni, Dalung ya nisanta kan shi da jam’iyyar Kwankwaso, NNPP

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, a ranar Laraba ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina alakanta shi da sabuwar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Dalung, wanda ya yi wannan kiran a shafinsa na Facebook, ya bayyana kansa a matsayin jajirtaccen dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A kwanakin baya dai an alakanta tsohon ministan da jam’iyyar NNPP, kungiya ta uku da tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu fitattun ‘yan siyasa suka kafa gabanin zaben 2023.

Advertisement

Ya ce: “Ban san irin wannan yunkuri na siyasa ba. Akwai ƙungiyoyin haɗin gwiwar da dama da ke sake tsara dabarun tunkarar zaɓen shekarar 2023 bisa la’akari da rugujewar dimokuradiyyar cikin gida a cikin manyan jam’iyyun siyasa biyu. Harkar kasa tana daya daga cikin wadannan gungun ‘yan siyasa masu ra’ayi daya da manufar ceto dimokradiyya. Ni dai a gaskiya na san abin da ya shafi maslahar kasa ne ba burin siyasa na kowane dan kasa ba.

“Saboda haka, har da sunana a cikin Kwamitin Aiki na kasa na NNPP ba tare da izini ko tuntubar juna ba, wata muguwar dabara ce ta siyasa ta ‘yan siyasa masu son rai.

“Bari in sake nanata alkawuran na goyon bayan dan takarar shugaban kasa a kudancin kasar wanda ba zai wuce shekaru 60 ba. Na yi imanin cewa yana da amfani wajen tabbatar da gaskiya, daidaito, adalci, zaman lafiya da hadin kan yankin Kudancin Najeriya musamman matasa a 2023.”

Advertisement