Siyasa

Tsofaffin gwamnonin Bankin (CBN) 2 da suka shiga siyasa, Kuma suka ci zabe a matsayin gwamnoni

Clement Isong da Charles Soludo

Wadannan mutane biyu sun rike mukamai a matsayin Gwamnonin Babban Bankin Najeriya, kuma daga baya suka shiga siyasa suka ci zabe a matsayin gwamnonin jihohinsu.

1. Clement Isong;
Ya taba rike mukamin gwamnan CBN daga shekarar 1976 zuwa 1975, a lokacin mulkin soja na Yakubu Gowon. Isong yana da Ph.D. a fannin tattalin arziki kuma ya koyar da tattalin arziki a jami’ar Ibadan kafin ya koma CBN. Ya kuma yi aiki a Asusun Ba da Lamuni na Duniya a matsayin mai ba da shawara a sashen Afirka. Isong ya jagoranci CBN a lokacin yakin basasar Najeriya (Yuli 1967-Janairu 1970).

Bayan ya yi ritaya daga CBN, ya shiga harkokin siyasa, aka zabe shi a matsayin gwamnan zartaswa na farko a jihar Kuros Riba daga 1979 zuwa 1983 a karkashin jam’iyyar National Party of Nigeria. Ya mutu a ranar 29 ga Mayu, 2000.

Advertisement

2. Charles Soludo;
Soludo Farfesa ne a fannin tattalin arziki kuma tsohon gwamnan CBN. Ya zama gwamnan babban bankin kasa CBN ne a shekarar 2004 bayan ya dan yi aiki a matsayin babban mai baiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara kan tattalin arziki, wanda kuma ya nada shi a matsayin shugaban babban bankin. Nasarar da Soludo ya samu a babban bankin kasar CBN ita ce manufar karfafa tsarin banki. Manufofin sun ga adadin bankunan Najeriya sun ragu sosai amma tare da karin karfi da kwarin gwiwa a bangaren banki bayan aikin.

A halin yanzu shi ne zababben gwamnan jihar Anambra bayan ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 6 ga Nuwamba, 2021. Za a rantsar da shi a ranar 7 ga Maris, 2022.

Advertisement