Kannywood
Trending

Tirkashi Rayya Ta Shirin Kwana Casa’in Ta Nemi Shiga Cikin Shirin Nan Da Ake Badala BBNaija Harma Ta samu gayyatarsu

Kiris ya rage ma’abota kallo su ga jaruma fim mai dogon zango na Kwana Casa’in, Jaruma Surayya Aminu, tsamo-tsamo a cikin shirin BBnaija na wannan shekarar.

Wannan shirin dai yafi farin jini ga ‘yan kudancin Najeriya kuma hatta mabiya addinin Kirista suna kira ga mabiyansu da su nisanci shirin sakamakon tsagwaron badala da ake nunawa.

Har ila yau, a shirin babu zancen addini domin babu masallaci ko coci na tsawon watanni uku zuwa hudu, inda ake cigaba da shirin ana zabe tare da zare mutane.

Daga bisani, wanda ya zama zakaran gwajin dafin shirin na tafiya da manyan kyautuka kamar miliyan dari, mota da sauransu.

Tirkashi Rayya Ta Shirin Kwana Casa'in Ta Nemi Shiga Cikin Shirin Nan Da Ake Badala BBNaija Harma Ta samu gayyatarsu

A wallafar da jaruma Rayya tayi a shafukanta na Instagram da TikTok, ta bayyana sakon da mashiryan shirin suka turo mata bayan ta shiga tantancewar shirin har ta samu nasara.

Sai dai kash, rashin duba sakonninta na Email yasa bata ga gayyatar da suka turo mata ba sai daga bisani.

➡️Bidiyon Yadda Wani Karamin Yaro Yahau Saman Fly-Over Yace Bazai Sauko ba Harsai Buhari Ya Sauka Daga

Back to top button